19 Yuli 2026 - 18:04
Source: ABNA24
Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Gaza; Wasu Da Dama Sun Yi Shahada Da Jikkata

A daidai lokacin da ake ci gaba da rikici a zirin Gaza, hare-haren sojojin gwamnatin yahudawa a yankuna daban-daban na wannan ziri a cikin dare da rana da suka gabata, sun haifar da shahada da jikkatar wasu 'yan ƙasar Falasdinu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin Falasdinu sun sanar da cewa, a hare-haren manyan bindigogi da na sama na sojojin gwamnatin yahudawa a unguwar "Al-Zaytun" a kudancin birnin Gaza, Falasdinawa da dama sun yi shahad kuma wasu sun jikkata. Haka kuma, a harin da aka kai wa wani gidan zama a yammacin birnin Gaza, da kuma wani harin bama-bamai a wani gida a unguwar "Al-Nasr," wasu fararen hula da dama sun yi shahada wasu kuma sun jikkata. A arewacin zirin Gaza ma, wani Bafalasdine ya rasa ransa sakamakon harbin sojojin Isra'ila a yankin "Al-Furushiya," kuma wani matashi ya rasa ransa sakamakon raunukan da ya samu a hare-haren baya.

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa tun daga farkon tsagaita wuta zuwa yanzu, adadin wadanda abin ya shafa ya kai shahidai 1,147 da raunata 3,703. Wannan ma'aikatar ta kuma sanar da cewa tun daga farkon yaƙi a ranar 7 ga Oktoba 2023 zuwa yanzu, adadin shahidan Gaza ya kai 73,269, kuma adadin raunata ya kai 173,811.

………………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha